An Kai Hari Kusa Da Karamin Ofishin Jakadancin Amurka A Jeddah
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7606-an_kai_hari_kusa_da_karamin_ofishin_jakadancin_amurka_a_jeddah
Rahotanni daga Saudiyya na cewa wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kan sa cikin mota a kusa da karamin ofishin jakadancin Amurka na Jeddah.
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 04, 2016 00:31 UTC
  • An Kai Hari Kusa Da Karamin Ofishin Jakadancin Amurka A Jeddah

Rahotanni daga Saudiyya na cewa wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kan sa cikin mota a kusa da karamin ofishin jakadancin Amurka na Jeddah.

Harin dai ya auku ne jim kadan da fara sallar Asuba a wannan safiyar ta Litinin a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar cikin gidan Saudiyya.

Sanarwar ta ce jami'an tsaro sun killace wurin da lamarin ya auku saidai an samu jami'an tsaro biyu da suka jikkata a wannan harin da bai yi nasara ba.

Har yanzu dai ba'a bayyana asalin mutumin da ya kai harin ba ko kuma manifar sa, aman an ce ya kai harin ne a wurin ajiye motoci na asibitin unguwar dake kusa da karamin ofishin jakadancin na Amurka.

Wannan harin dai ya zo ne a wannan ranar ta hudu ga watan Yuli data yi daidai da ranar samun incin kai ta Amurka wato '' l'Independence Day''.

Wata sanarwa daga gwamnatin Washington ta bakin kakakin ta ta tabbatar da aukuwar lamarin, tare da cewa duk ma'aikatan difolmatsiyar ta na cikin koshin lafiya.