Kuwait : An Dakile Hare-haren (IS) Guda Uku
(last modified Mon, 04 Jul 2016 05:01:59 GMT )
Jul 04, 2016 05:01 UTC
  • Kuwait : An Dakile Hare-haren (IS) Guda Uku

Ma'aikatar cikin gida a Kuwait ta sanar da yin nasarar dakile hare-hare 'yan ta'ada na (IS) har guda uku a ciki kasar.

Hakan dai a cewar ministan harkokin cikin gidan kasar ya biyo bayan samame da jami'an tsaro suka kai a wasu wurare uku a cikin kasar inda aka cafke wasu mutane biyar da ake zargi, kuma cikinsu harda wani dan sanda da wata mata, wadanda duk 'yan asalin kasar ta Kuwait ne.

Bayanan da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar sun ce mutanen na shirin kai hare-hare a kasar a wurare da dama ciki har da aniyar tayar da bam a wani masallacin 'yan Shi'a.

kazalika a cewar sanarwar duka mutanen da aka cafke sun amsa laifin da ake zargin su na alaka da kungiyar (IS), aman 'yan sanda kasar na ci gaba da neman wani mutume dan asalin yankin Gulf da kuma Asiya da ba'a bayyana ba wanda yake taimakawa mutanen wajen shirin kai hare-haren.

Wannan sanarwar na zuwa ne shekara guda bayan da wani dan kunar-bakin-wake dan asalin kasar Saudiya ya tarwatsa kansa a wani masallacin Shi'a a Kuwaitin, inda ya kashe mutum 27.