Yamen: Hare-haren Saudiyya
Jul 08, 2016 14:29 UTC
Jiragen Yakin Saudiyya na ci gaba da kai hare-hare a kasar Yamen.
Jiragen yakin Saudiyya na ci gaba da kai hare-hare a kasar Yamen.
Tashar Telbijin din al-alam mai watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran, ta ambato majiyar tsaron Yamen, da ke nuni da kai hare-hare har sau 31 da jiragen yakin Saudiyya su ka yi.
Haren-haren na yau dai sun kunshi yankunan Hajjah, da Ma'arib da Sa'adah da San'aa.
Shekaru biyu kenan a jere da Saudiyyar ta shelanta yaki akan kasar Yamen, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma jikkata wasu.
Tattaunawar sulhu da ake yi a kasar Kuwaiti ba ta harfar da Da, mai ido ba har yanzu.
Tags