Turkiyya : Mutane 37 Ke Tsare Bisa Zargin Harin Santambul
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7936-turkiyya_mutane_37_ke_tsare_bisa_zargin_harin_santambul
Rahotanni daga Turkiyya na cewa an sake cafke wasu mutane bakwai 'yan asalin kasashen waje bisa zargin su da alaka da kungiyar IS da kuma hannu a jerin hare hare filin jirgin saman Ataturk na Santambul.
(last modified 2018-08-22T11:28:34+00:00 )
Jul 11, 2016 12:36 UTC
  • Turkiyya : Mutane 37 Ke Tsare Bisa Zargin Harin Santambul

Rahotanni daga Turkiyya na cewa an sake cafke wasu mutane bakwai 'yan asalin kasashen waje bisa zargin su da alaka da kungiyar IS da kuma hannu a jerin hare hare filin jirgin saman Ataturk na Santambul.

Kawo yanzu adadin mutanen da aka cafke kuma ma'aikatar shari'a kasar ke zargi da hannu a hare-haren na ranar 28 ga watan jiya ya kai 37.

A jumulce dai 'yan kasashen waje 22 ne da kuma 'yan kasar ta Turkiyya 15 ne ake tsare da bisa wannan zargin.

Abun rikewa dai anan shi ne har yanzu babu kungiyar data dau alhakin kai harin na baya bayan nan wanda ya kasance mafi muni a cikin jerin hare-haren da kasar ta Tukiyya ta fuskanta a cikin wannan shekara.