Rikicin Turkiya Da Kurdawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i799-rikicin_turkiya_da_kurdawa
Turkiya Ba Za ta bari Garin A'azaz ya shiga karkashin Ikon Kurdawa ba.
(last modified 2018-08-22T11:27:49+00:00 )
Feb 15, 2016 13:24 UTC
  • Rikicin Turkiya Da Kurdawa

Turkiya Ba Za ta bari Garin A'azaz ya shiga karkashin Ikon Kurdawa ba.

Gwamnatin kasar Turkiya ta bakin ministan harkokin wajenta, Ahmad Daud' Oglu ta sanar da cewa ba za ta bari gari A'azaz da ke cikin Syria ya shiga karkashin ikon Kurdawa ba.

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyan ya fadi haka ne a yau litinin, a matsayin maida martanin da ya ke yi akan dalilan da su ka sa sojojin kasarsa su ka kai hare-hare a cikin iyakar kasar Syria.

Ahmad Daud Oglu ya ci gaba da cewa; Kasar tasu ba kuma za ta bari yankuan Afrin da ke gabacin kasar ba ya shiga karkashin ikon mayakan kurdawa.

A cikin kwanaki biyu da su ka gabata sojojin na Kurdawa sun kai hare-hare da manyan bindigogi a cikin kasar Syria.