Kusan Mutane 6000 Aka Kame A Turkiya Akan Batun Juyin Mulki.
Jul 18, 2016 17:50 UTC
Kusan Mutane 6000 Aka Kame A Turkiya Akan Batun Juyin Mulki.
Jami'an gwamnati a Turkiya sun sanar da cewa ya zuwa jiya lahadi, an kame kusan mutane 6000 masu hannu a juyin mulki.
Ministan shari'a na kasar Turkiyan, ya kuma yi gargadin cewa adadin mutanen da za a kama zai iya karuwa nan gaba.
A gefe daya, ministan tsaron kasar Turkiya ya ce; An dakile, juyin mulki, sai dai har yanzu ana fuskantar hatsari.
A jiya lahadi ne dai shugaban kasar Rajab Tayyib Urdugan ya ce; Wajibi ne kasar ta yi amfani da hukuncin kisa akan wadanda su ka kitsa juyin mulkin.
Tags