An kafa Dokar Ta-baci A Turkiyya
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan Ya kafa dokar ta-baci, ta tsawan watanni uku bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar.
Wannan matakin dai a cewar Erdogon domin a samu damar ladabtar da wadanda ke da hannu a cikin yunkurin juyin mulkin da ya cutura a makon jiya.
Erdogan ya bayana hakan da yammacin jiya Laraba bayan wani taron majalisar tsaron kasar da kuma na majalisar ministocinsa wanda yayi na'am da matakin kafa dokar ta bakin.
hakazalika a cewar shugaban wannan matakin zai sanya a kawar duk wasu mambobi na wata kungiya yan ta'ada dake da hannu a yunkurin neman kifar da tsarin demokuradiyya a kasar.
A cikin jawabinsa Erdogan ya kuma kara da cewa matakin kada dokar ta bakin ba wai nayi ma tsarin demokuradiyya illa ba ne, A'a na kare al'umma ne da kuma samar masu da walwala a cikin kasa.