Turkiyya : Erdogan Zai Gana Da Manyan 'Yan Adawan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8635-turkiyya_erdogan_zai_gana_da_manyan_'yan_adawan_kasar
Shugaba Recep Tayyip Erdogan, na kasar Turkiyya zai gana da mayan 'yan adawa na kasar yau Litinin, inda zai tattauna dasu akan yunkurin yujin mulkin kasar da baiyi nasara ba.
(last modified 2018-08-22T11:28:39+00:00 )
Jul 25, 2016 06:50 UTC
  • Turkiyya : Erdogan Zai Gana Da Manyan 'Yan Adawan Kasar

Shugaba Recep Tayyip Erdogan, na kasar Turkiyya zai gana da mayan 'yan adawa na kasar yau Litinin, inda zai tattauna dasu akan yunkurin yujin mulkin kasar da baiyi nasara ba.

Mr Ergodan da firayi ministansa Binali Yildirim, zasu gana da jagororin jam'iyun adawa na kasar da suka hada da Kemal Kiliçdaroglu, na (CHP), da Devlet Bahceli, na (MHP), kuma zasu tattauna batutuwa da dama da suka shafi yunkurin juyin mulkin da kula illarsa ga kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da masu mulki da 'yan adawa na kasar zasu zauna waje daya tun bayan juyin mulkin da ya cutura a wannan kasa.

Dama kafin hakan 'yan adawa na kasar sun gudanar da wata zanga zanga a jiya lahadi, ta yi allawadai da yunkurin juyin mulkin.

Zanga-zangar dai ta jiya ta zo ne kwanaki takwas bayan yunkirin kifar da gwamnatin ta Erdogan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 270, da kuma kame-kame mutane masu yawa da suka da sojoji da ma'aikatun shari'a, dana makakarantu da kuma na jarida.