Kasar Italiya Ta Bukaci Sanya Matsin Lamba Kan Gwamnatin Turkiyya
Ministan harkokin wajen kasar Italiya ya bukaci daukan matakin sanya matsin lamba kan gwamnatin Turkiyya domin ta mutunta dokokin kasar a kokarin da take yi na daukan fansa kan masu yunkurin juyin mulki da bai yi nasara.
A jawabinsa a gaban Majalisar Dokokin Kasar Italiya a jiya Talata: Ministan harkokin wajen kasar ta Italiya Paolo Gentiloni ya bayyana cewa a bisa la'akari da yadda gwamnatin Turkiyya take tsananta daukan mataki kan mutanen da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki a kasar, ya zame dole a dauki matakin matsin lamba kanta domin ta mutunta tsarin dokokin kasar.
Gentiloni ya kara da cewa: Irin mummunan martanin da gwamnatin Turkiyya musamman shugaban kasar Rajab Tayyib Erdogan ke son dauka a kan yunkurin juyin mulkin yana neman wuce gona da iri saboda ga dukkan alamu ana neman hanyar da zata kai ga zartar da hukuncin kisa kan mutanen da ake zargi da yunkurin juyin mulkin kuma hakan ba karamin abin tashin hankali ba ne.
Tun bayan yunkurin juyin mulki a ranar 15 ga wannan wata na Yuli da bai kai ga samun nasara a Turkiyya ba, mahukuntan kasar suka kame mutane da yawansu ya haura 60,000 da suka hada da sojoji, ma'aikatan gwamnati, alkalai da sauransu, baya ga koran mutane daga aiki da dakatar da wasu na daban.