Fashewar Bom ya gilgiza Birnin Ankara na Kasar Turkiya
Tashin Bom Ya gilgiza Ankara babban birnin kasar Turkiya
Kamfanin dillancin labaran CNN Turk ya habarta Bom din ya tashi ne a gidan kwana na sojojin kasar a yau Laraba, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5 tare da jikkata wasu 10 na daban.
Rahoton ya ce harin ya auku ne a kusa da Majalisar Dokokin kasar da kuma Ma'aikatar babban hafsan sojojin kasar
A cewar Muhamad Kalich lar Gwamnan Birnin Ankara bashewar Bom din ya yi kama da irin harin bom din da aka 'yan ta'adda suka saba kaiwa na sanya bama-bama a cikin Mota.
A nasa bangare Piraministan kasar Ahmat Auglo ya yi alawadai da wannan hari tare kuma da bayyana shi a matsayin ta'addanci sannan kuma ya kara da cewa suna gudanar da bincike domin gwano wadanda suka kai wannan hari na ta'addanci.