Rasha Ta Karyata Shigar Jirginta na yaki Sararin samaniyar kasar Turkiya.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i94-rasha_ta_karyata_shigar_jirginta_na_yaki_sararin_samaniyar_kasar_turkiya.
Rasha Ta karyata cewa jirginta na yaki ya kutsa sararin samaniyar kasar Turkiya
(last modified 2018-08-22T11:27:44+00:00 )
Feb 01, 2016 18:06 UTC
  • Rasha Ta Karyata Shigar Jirginta na yaki Sararin samaniyar kasar Turkiya.

Rasha Ta karyata cewa jirginta na yaki ya kutsa sararin samaniyar kasar Turkiya

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta fitar da bayani a yau litinin da a ciki ta kore abinda kasar Turkiya ta ambata na cewa; jiragen yakin kasar sun kutsa sararin samaniyar kasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha Igor Konashinkov ya bayyana baynin na Turkiya da cewa tsokana ce ta ganganci, sannan ya kara da cewa; babu kamshin gaskiya a ciki."

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar ta Rasha ya ci gaba da cewa; sun sami hotuna da su ke nuna yadda manyan bindigogin Turkiya su ke kai hari a cikin wasu kauyuka da ke cikin kasar Rasha, saboda haka sun bukaci cikakken bayani daga kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.

Tun da fari dai kasar Turkiya ta bayyana cewa jirgin yakin Rasha ya shiga cikin iyakarta ta sama, abinda ya jawo suka da yin Allah wadai daga kungiyar tsaro ta Nato, wacce Turkiyan ta ke a matsayin memba a cikinta.