Rasha Ta Kai Hari cikin Siriya Tun Daga Iran
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i9724-rasha_ta_kai_hari_cikin_siriya_tun_daga_iran
karon farko jiragen yakin Rasha sun kai hari kan cibiyoyin 'yan ta'ada a Siriya tun daga sansanin jiragen sama a arewa maso yammacin Iran.
(last modified 2018-08-22T06:58:46+00:00 )
Aug 16, 2016 06:45 UTC
  •  Rasha Ta Kai Hari cikin Siriya Tun Daga Iran

karon farko jiragen yakin Rasha sun kai hari kan cibiyoyin 'yan ta'ada a Siriya tun daga sansanin jiragen sama a arewa maso yammacin Iran.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro Rasha ta fitar a yau ta ce jiragen yakin ta kira Tu-22M3 da Su-34, sun tashi daga karamin filin jirgin Hamedan a Iran kuma sun kai hari a wasu cibiyoyin 'yan ta'addan (IS) da Al'nosra a jihohin Aleppo da Deir Ezzor da kuma Ibled.

Sanarwar ta kara da cewa an tarwasa wasu wurare biyar na adanon makamai da atisaye 'yan ta'addan a Deir Ezzor .

hakazalika a cewar sanarwar jiragen Rasha sun tarwasa  wasu wurare uku inda 'yan ta'ada ke shirye kai hare-hare a jihar Jafar da Deir Ezzor tare da hallaka dayewa daga cikin 'yan ta'adan.