Harin Bom Ya Kashe Mutane Uku A gabashin Turkiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i9805-harin_bom_ya_kashe_mutane_uku_a_gabashin_turkiyya
Rahotanni daga Turkiyya na cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu kana wasu 120 suka jikkata a wani harin bom da aka kai a gabashin kasar.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Aug 18, 2016 09:30 UTC
  • Harin Bom Ya Kashe Mutane Uku A gabashin Turkiyya

Rahotanni daga Turkiyya na cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu kana wasu 120 suka jikkata a wani harin bom da aka kai a gabashin kasar.

Bayani sun nuna cewa ganin yawan mutane da suka jikkata, mai yiwa adadin wadanda suka rasa rayukan su ya karu.

Koda yake babu wata kungiya data dau alhakin kai harin, aman tuni aka fara alakanta harin da na kungiyar Kurdawan nan ta PKK.

Ko a cikin daren jiya Laraba ma wata mota makkare da boma bomai ta tarwatse a gaban shalkwatar 'yan sanda birnin Van dake gabashin kasar ta Turkiyya inda mutane uku suka mutu wasu 73 kuma suka jikkata.