Majalisar Dokokin Turkiyya Ta Amunce Da Dawo Da Alaka Da Israila
Majalisar dokoki a Turkiyya ta amunce da dawo da huldar diflomatsiya da Israila, bayan shafe shekaru shida na rashin jituwa.
A karshen watan Yuni daya gabata ne kasashen biyu suka cimma matsaya ta dawo da hulda tsakaninsu, kafin daga bisani a mika kudirin ga majalisar dokokin kasar wace ta amunce dashi a cikin daren jiya Juma'a.
A bisa yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma, Israi'la zata biya Turkiyya diyya ta kudade da yawan su ya kai $ Amurka Miliyan 20 bayan wani farmaki da Israila ta kaiwa wani jirgin ruwan kasar a gabar zirin Gaza a cikin shekara 2010, inda Turkiyawa 10 suka mutu.
Sannan a nata bangare ita kuwa Turkiyya zata janye tuhumar da take yiwa wasu tsaffin kwamandodin sojin Israi'a dake da hannu a farmakin na wacen lokacin.