Turkiyya : Mutane 50 Suka Mutu A Harin Gaziantep
Aug 21, 2016 11:57 UTC
Hukumomi a Turkiyya sun ce adaddin mutanen da suka mutu a harin da aka kai a wani taron buki a garin Gaziantep, ya kai 50.
koda yake babu wata kungiya data dau alhakin kai harin aman tuni hukumomin kasar a sahun gaba shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya dangantasa ga kungiyar nan ta 'yan ta'addan IS.
An dai kai harin ne a daidai kan iyakan kasar da Syria.
Gwamnan yankin Ali Yerlikaya ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa adadin mutanen da suka mutu ya karu sabanin 30 na farko da aka sanar.
Tags