-
Al'ummar Kasar Girka Sun Yi Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kashe Musulmin Myanmar
Sep 17, 2017 02:03Al'ummar Girka karkashin jagorancin kungiyoyin kare hakkin bil-Adama na kasar sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da kisan gillar da ake yi wa al'ummar musulmin kasar Myanmar ko kuma Burma.
-
Fira Ministan Iraki Ya Yi Gargadin Daukan Matakin Soji Kan Yankin Kurdawan Kasar
Sep 17, 2017 02:02Fira ministan Iraki ya gargadi mahukuntan yankin Kurdawan kasar da cewa matukar aniyarsu ta gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan neman ballewa daga kasar Iraki ta haifar da bullar rikici a kasar, to babu makawa gwamnatin Iraki zata dauki matakin soji domin dakatar da lamarin.
-
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula A Lardin Ta'az Na Kasar Yamen
Sep 16, 2017 07:22Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai jerin hare-haren wuce gona da iri kan lardin Ta'az da ke shiyar kudu maso yammacin kasar Yamen, inda suka kashe fararen hula akalla takwas tare da jikkata wasu da dama.
-
Kasashen Sudan Da Qatar Sun Jaddada Muhimmancin Karfafa Alaka A Tsakaninsu
Sep 16, 2017 07:21Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ya bada labarin cewa: Mahukuntan Sudan da Qatar sun tattauna kan hanyoyin bunkasa alaka tare da taimakekkeniya a tsakaninsu.
-
Iraki : An Tsige Gwamnan Kirkuk
Sep 14, 2017 12:02Majalisar tarayya a Iraki ta amunce da gagarimin rinjaye da tsige gwamnan yankin Kirkuk, Najm Eddine Karim saboda nuna goyan bayansa ga kiran zaben raba gardama na kafa kasar Kurdawa.
-
Iraki : Hare-hare IS Sun Yi Ajalin Mutum A Kalla 52
Sep 14, 2017 11:33Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh ta dauki alhakin kai jerin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a kalla 52 a kusancin Bagadaza babban birnin kasar.
-
Saudiyya Tana Kokarin Hana Gudanar Da Bincike Kan Ayyukan Ta'addancinta A Kasar Yamen
Sep 14, 2017 07:28Wakilin kasar Saudiyya a kwamitin kolin kula da kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci yin watsi da batun gudanar da bincike kan cin zarafin bil-Adama a kasar Yamen.
-
Yemen: An Yi Tattaunawa A Tsakanin Tsohon Shugaban Kasa Abdallah Saleh Da Jagoran 'Yan Huthi.
Sep 13, 2017 14:29Tattaunawar a tsakanin Abdulmalik Badruddin al-huthy da Ali Abdullah Saleh ta maida hankali ne akan dinke barakar da ke tsakaninsu domin kalubalantar makiya.
-
Fira Ministan Iraki Ya Ce Shirin Ballewar Yankin Kurdawa Daga Kasar Ya Saba Doka
Sep 13, 2017 07:50Fira ministan Iraki ya jaddada cewa: Shirin gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a da mahukuntan yankin Kurdawar kasar ke yi dangane da neman ballewa daga kasar ta Iraki ya sabawa doka.
-
Wasu Kasashen Larabawa Sun Yanke Taimakon Kudin Da Suke Baiwa Gwamnatin Palastinu
Sep 13, 2017 01:22Wasu daga cikin kasashen Larabawa su kudiri yanke taimakon kudaden da suke bawa gwamnatin Palastinu daga watan oktoba mai kamawa.