-
Jami'an Tsaron Saudiya Sun Kashe Daya Daga Cikin Mazauna Yankin Awamiya Dake Gabashin Kasar
Aug 04, 2017 14:30Bayan da jami'an tsaron saudiya suka bindige daya daga cikin mazauna yankin awamiya a wannan juma'a, adadin mutane da aka kashe a wannan yanki ya haura zuwa shida.
-
Dakarun Hizbullah 5 Da Jabhatun Nusra Ta Sace Sun Dawo Gida
Aug 04, 2017 06:08Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewa ana ci gab da gudanar da bukukuwan farin ciki don maraba da dakarun kungiyar Hizbullah na kasar su 5 da suka dawo gida bayan sama da shekara guda a hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra' da ke da alaka da kungiyar Al-Qa'ida.
-
Yahudawa Na Shirin sake Afka Wa Masallacin Aqsa
Aug 03, 2017 12:56Wata kungiyar yahudawa masu tsatsauran ra'ayi ta kirayi sauran yahudawa domin su hada karfi da karfe domin kaddamar da farmaki a kan masallaci aqsa mai alfarma.
-
Saudiyya: Jami'an Tsaro Na Ci Gaba Da Kai Hari A Birnin Awamiyya
Aug 03, 2017 02:07Sojojin Saudiyya sun sake aikewa da kayan yaki zuwa garin Awamiyya tare da tsananta hare-hare akan fararen hular da su ke cikinsa.
-
Yan Ta'adda Sun Kai Hari Da Makami Mai Linzami Kan Ofishin Jakadancin Rasha Da Ke Kasar Siriya
Aug 02, 2017 13:45Kungiyoyin 'yan ta'adda sun kaddamar da harin wuce gona da iri da makami mai linzami kan ofishin jakadancin kasar Rasha da ke birnin Damasqas fadar mulkin kasar Siriya a yau Laraba.
-
An Fara Musayen Fursunoni Tsakanin Hizbullah Da Jabhatun Nusra
Aug 02, 2017 06:35Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewar an fara aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon din da kungiyar ta’addancin nan ta Jabhatun Nusrah, inda ‘yan ta’addan suka sako wasu dakarun kungiyar Hizbullah din su uku da suka kama a bangare guda kuma gwamnatin Labanon din ta sako ‘yan kungiyar su uku da take tsare da su.
-
Sojojin Yemen Sun Mayar Da Martani A Kan Ta'addancin Saudiya
Aug 02, 2017 02:02Sojoji da Dakarun sa kai na kungiyar Ansarullah na kasar yemen sun kai hari wuraren taruwar sojojin hayar saudiya a yankunan Asir, Jauf da Ta'az tare da hallaka da dama daga cikin su.
-
Afganistan : Hari Ya Salwantar Da Rayukan Mutane Sama Da 20 A Masallaci
Aug 01, 2017 13:22Rahotanni daga Afganistan na cewa sama da mutane 20 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a masallacin Herat dake yammacin kasar.
-
Pakistan : An Zabi Shahid Khaqan Abbasi A Matsayin Sabon Firaminista
Aug 01, 2017 12:16Majalisar dokoki a Pakistan ta zabi Shahid Khaqan Abbasi a matsayin sabon Firaminista bayan kotun kolin kasar ta tube Nawaz Sharif kan badakalar rashawa a makon jiya.
-
Qatar Ta Zargi Saudiyya Da Saka Siyasa A Cikin Harkokin Aikin Hajji
Aug 01, 2017 00:29Hukumomin Qatar sun zargi Saudiyya da saka siyasa a cikin harkokin addini lamarin dake kawo cikas ga aikin hajji.