-
Kungiyar Hamas Ta Bukaci Ci Gaba Da Kokarin Kare Masallacin Qudus
Jul 31, 2017 01:49Shugaban bangaren siyasar kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ya jaddada bukatar ci gaba da kokarin kare birnin Qudus da Masallacin Aksa daga mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Syria: Kungiyoyin 'Yan ta'adda A Halab Sun Kai Wa Junansu Harin Kunar Bakin Wake.
Jul 30, 2017 14:33Kungiyar Da'esh ko Isil ce ta kai harin kunar bakin wake akan 'yan kungiyar "Nusra" da su ke taro da kungiyar Ahrarush sham a kusa da Halab.
-
Saudiyyah: Jami'an Tsaron Al Saud Sun Kashe Fararen Hula 5 A Yankin Qatif
Jul 28, 2017 14:24Rahotanni daga yankunan gabashin kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa a cikin kwanaki biyu jami'an tsaron masarautar iyalan gidan saud sun kasashe fararen hula 5 a yankin Qatif ba tare da bayyani wani dalili na yin hakan ba.
-
Yemen: Makamai Masu Linzami Sun Sauka Akan Sansanin Sojan Saudiyya Da Ke Ta'if.
Jul 27, 2017 23:33Sojojin Kasar Yemen sun harba makamai masu linzami akan sansanin sojan saman Saudiyya da ke birnin Ta'if a yammacin kasar.
-
Sallar Juma'a A Masallacin Kudus Cikin Zaman Dar-dar
Jul 27, 2017 23:33Bayan shafe kwanaki 15 na kaucewa sallah a cikin masallacin Kudus, ana sa ran Palasdinawa zasu gudanar da Sallar Juma'a a harabar masallacin.
-
Al Saud Na Ci Gaba Da Kaddamar Da Farmaki Kan Al'ummar Awamiyyah
Jul 27, 2017 07:51Jami'an tsaron masarautar Al Saud suna ci gaba da kaddamar da farmaki a kan al'ummar birnin Awamiyyah da ke cikin gundumar Qatif a gabashin Saudiyyah.
-
An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Hizbullah Da 'Yan Ta'adda
Jul 27, 2017 07:47Rahotanni daga kasar Lebanon sun sheda cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun Hizbullah da kuma 'yan ta'addan takfiriyyah na Jabhat Nusra.
-
Red Cross Ta Bukaci Kasashen Duniya Da Su Taimaka Wajen Kawo Karshen Yakin Saudiyya A Kan Yemen
Jul 27, 2017 00:57Kungiyar Red Cross ta duniya (ICRC) ta bukaci kasashen Yammaci da na yankin Gabas ta tsakiya da su yi amfani da irin tasiri da karfin da suke da shi wajen kawo karshen wuce gona da irin da Saudiyya take yi a kan al'ummar kasar Yemen.
-
Sayyid Nasrallah: Hizbullah Sun Kwato Kusan Dukkanin Yankunan Labanon Dake Hannun Jabhatun Nusra
Jul 27, 2017 00:56Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar dakarun kungiyar sun kusa kwato dukkanin yankunan kasar Labanon da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra suke rike da su tsawon shekaru, yana mai jinjinawa irin namijin kokarin da dakarun kungiyar da sojojin Labanon suka yi wajen cimma wannan nasarar.
-
'Yan Taliban Sun Kashe Sojojin Afganistan 26
Jul 26, 2017 10:08Hukumomi a Afganistan sun ce sojojin kasar 26 ne suka rasa rayukansu a yayin wani hari da mayakan Taliban suka farma wa sansaninsu dake kudancin kasar.