-
Irakawa Akalla 11 Ne Suka Yi Shahada A Wani Ta'addanci Da Aka Kai Kasar Iraki
May 30, 2017 02:25Harin ta'addanci ta hanyar tarwatsa wata mota da aka makare da bama-bamai a yankin Karadah da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki yayi sanadiyar shahadar mutane akalla 11 tare da jikkatan wasu fiye da 50 na daban.
-
A Yayin Da Ake Shirye Shiryen Yanto Jihar Nainuwa, Firaministan Iraki Ya Kai Ziyara Birnin Mausil
May 29, 2017 13:46A yayin da Dakarun sa kai na Hashadu-Sha'abi suka isa kan iyakar kasar Iraki da Siriya dake yammacin jihar Nainuwa na arewacin kasar, Firaminstan kasar Haidar Abadi ya shiga birnin Mausil babban birnin Jihar Nainuwa a marecen wannan Litinin.
-
Karancin Magunguna Yana Barazana Ga Rayukan Kananan Yara A Yankin Zirin Gaza
May 28, 2017 14:40Majiyar Lafiya a Yankin Zirin Gaza da ke Palasdinu ta sanar da cewa: Matsalar karancin magunguna da kayayyakin aiki suna barazana ga rayukan kananan yara a yankin.
-
Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Gano Hanyoyin Karkashin Kasa Da 'Yan Ta'adda Suke Amfani Da su
May 28, 2017 14:37Sojojin gwamnatin Siriya suna ci gaba da tsarkake yankunan Wa'ar da ke garin Homs daga gungun 'yan ta'adda, inda suka gano tarin hanyoyin karkashin kasa da 'yan ta'adda suke amfani da su.
-
Akalla Mutane 16 Sun Rasa Rayukansu A Wasu Hare-Hare A Lardin Dayala Na Iraki
May 28, 2017 06:41Wasu munanan hare-haren ta'addanci da aka kai a yau a garin Ba'akuba da ke cikin lardin Dayala da ke Iraki, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 16 tare da jikkatar wasu.
-
Saudiya Ta Koro 'Yan Ghana 5,00
May 27, 2017 12:59Mahukuntan Saudiyya sun dauki matakin tuso keyar wasu 'yan kasar Ghana su kimanin 5,00 wadanda ke rayuwa a kasar ba bisa ka'ida ba.
-
Pakistan Ta Sake Bude Iyakarta Da Afganistan
May 27, 2017 10:57Hukumomi a Pakistan sun sanar da sake bude iyakar kasar da Afganistan a dalilin watan Azumin Ramadana, makwanni kadan bayan arangamar data wakana tsakanin sojojin kasashen biyu.
-
IS Ta Dauki Alhakin Kai Hari Kan Kifdawa A Masar
May 27, 2017 09:36Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta ce ita keda alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar Kristocin Kifdawa 29 a birnin Minya dake tsakiyar kasar Masar.
-
Fursunonin Palastinawa Sun Dakatar Da Yajin Cin Abinci
May 27, 2017 07:37Palastinawan da ke yajin cin abinci a gidajen kason Isra'ila sun kawo karshen yajin cin abincin nasu a yau bayan cimma yarjejeniya kan hakan.
-
IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin Indonusiya
May 26, 2017 03:49Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai tagwayen hare haren da sukayi sanadion mutuwar 'yan sanda uku a birnin Jakarta na kasar Indonusiya.