-
Dakarun tsaron Iraki sun hallaka 'yan ta'adda da dama a kudancin Mosil
Oct 21, 2016 14:21Sama da 'yan ta'adda 200 suka hallaka a ci gaba da farmakin da sojojin Iraki ke kaiwa 'yan ta'addar IS domin tsarkake jihar Mosil.
-
Sojojin Gwamnatin Iraki Suna Ci Gaba Da 'Yantar Da Yankunan Garin Mosel Daga 'Yan Ta'adda
Oct 21, 2016 01:50A cikin kwanaki hudu da fara kaddamar da hare-haren soji kan garin Mosel da ke lardin Nainawa na kasar Iraki da nufin 'yantar da garin daga mamayar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish, sojojin gwamnatin Iraki sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa gami da kwato yankuna da dama.
-
Sojojin Yamen Sun Kashe Sojojin Mamayar Saudiyya Da Dama A Arewa Maso Yammacin Kasar
Oct 21, 2016 01:24A wani sabon gumurzu da aka yi tsakanin sojojin kasar Yamen da sojojin mamayar masarautar Saudiyya a yankunan da suke arewa maso yammacin kasar ta Yamen; sojin Saudiyya da dama ne suka halaka, yayin da wasu adadi na daban suka jikkata.
-
Kungiyar Bada Agaji Ta Red Cross A Iraqi Ta Bukaci Ficewar Fararen Hula Daga Birnin Musil
Oct 20, 2016 14:20Komitin gudanarwa na kungiyar bada agaji ta Red Cross ta bukaci ficewar fararen hula daga birnin Musil na kasar Iraqi inda yaki mai tsanani yake gudana tsakanin mayakan daesh da sojojin kasar Iraqi
-
Shugaban Kasar Rasha Ya Amince Da Tsawaita Tsagaita Bude Wuta A Birnin Halab Na Tsawon Sa'oee 24
Oct 20, 2016 11:39Ministan tsaron kasar Rasha ya bayyana cewa shugaban kasar Vladmir Putin ya amince da tsawaita dakatar da bude wuta a birnin Halab na kasar Syria da sa'oee 24.
-
Putin Da Assad Sun Tattauna Kan Rikicin Syria Da Kuma Yaki Da Ta'addanci
Oct 20, 2016 02:16Shugabannin kasashen Rasha da Syria sun gudanar da wata tattaunawa a jiya ta wayar taroho, dangane da halin da ake ciki a Syria da kuma batun ci gaba da yaki da ta'addanci a kasar.
-
An Fara Aiki Da Shirin Dakatar Da Bude Wuta A Yemen
Oct 20, 2016 02:16Dukkanin bangarori sun fara aiki da shirin dakatar da bude wuta na kwanaki uku a kasar Yemen daga yau Alhamis, wanda za a iya kara tsawon wa'adinsa a lokuta masu zuwa.
-
Dakarun Iraki Na Samun Nasara A Yunkurinsu Na Tsarkake Mausul Daga 'Yan Ta'addan ISIS
Oct 20, 2016 02:15Dakarun gwamnatin Iraki tare da sojojin sa kai na al'ummar kasar Iraki suna ci gaba da samun samun gagarumar nasara a yunkurin da suke yi na tsarkake birnin Mausul daga 'yan ta'addan wahabiyawan takfiriyya na ISIS da ke rike da birnin tun shekaru biyu da suka gabata.
-
Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen Masar Da Siriya Kan Yaki Da Ta'addanci
Oct 19, 2016 02:23Majiyar watsa labaran Siriya ta bayyana cewa: A ziyarar aikin da shugaban cibiyar tsaron kasar Siriya Ali Mamluk ya kai zuwa kasar Masar; Kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu a fagen yaki da ta'addanci.
-
An Sanar Da Shirin Tsagaita Wuta A Yemen
Oct 18, 2016 14:47MDD, ta sanar da shirin tsagaita buda wuta na Sa’o’I 72 a kasar Yemen, wace za ta soma aiki daga ranar Alhamis mai zuwa.