-
Sojojin Siriya Sun Kwato Asibitin Garin Deir al-Zor Daga Hannun 'Yan Da'esh
May 15, 2016 00:53Sojojin Siriya sun sami nasarar kwace asibitin garin Deir al-Zor daga hannun 'yan kungiyar ta'addan nan Da'esh bayan wani gagarumin gumurzun da ya gudana tsakanin bangarori biyu a jiya Asabar bayan da 'yan ta'addan suka mamaye asibitin.
-
Rasha Ta Jaddada Muhimmancin Yanke Taimako Ga 'Yan ta'adda.
May 14, 2016 15:12Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana muhimmancin yanke hanyoyin taimakawa kungiyoyin ta'adda.
-
An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Allah Wadai Da Saudiyya A Yemen
May 13, 2016 13:19Dubun dubatan al'ummar kasar Yemen ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ta yin Allah wadai da gwamnatin Saudiyya da masu goya mata baya musamman Amurka saboda ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da suke yi a kasar, kamar yadda kuma suka jinjinawa dakarun kungiyar Ansarullah ('yan Houthi) da kuma sojojin gwamnatin saboda tsayin dakan da suke ci gaba da yi wajen tinkarar wannan wuce gona da irin.
-
Sheikh Na'im Qasim: Shahid Badrudden Ya Dandana Wa Isra'ila Da 'Yan Takfiriyya Kuda
May 13, 2016 12:35Na'ibin shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheik Na'im Qasim ya bayyana cewar babban kwamandan sojin kungiyar Shahid Mustafa Badruddeen wanda yayi shahada yau din nan a kasar Siriya ya dandana wa haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kungiyoyin 'yan takfiriyya masu kafirta musulmi kuda a kasar Siriyan yana mai cewa nan da wani lokaci kadan kungiyar za ta sanar da sakamakon binciken da ta gudanar dangane da harin da aka kai wa babban kwamandan da yayi sanadiyyar shahadarsa.
-
Kungiyar Da'ish Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Masu Amfani Da Wayar Hannu
May 13, 2016 06:45Kungiyar ta'addanci ta Da'ish mai kafirta musulmi tana ci gaba da aiwatar da ayyukan ta'addancinta kan al'ummar kasar Iraki.
-
Labanon : Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Babban Kwamandan Sojinta
May 13, 2016 01:01Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa babban kwamandan bangaren sojinta Shahid Mustafa Badruddeen yayi shahada sakamakon wani harin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wa daya daga cikin cibiyoyinta da ke kusa da filin jirgin saman birnin Damaskus na kasar Siriya.
-
Sojojin Hayar Masarautar Saudiyya Da Dama Sun Halaka A Kudancin Kasar Yamen
May 12, 2016 06:13Tashin wasu bama-bamai da aka bisine a kan hanyar shigewar rundunar mayakan tsohon shugaban kasar Yamen mai ritaya da sojojin hayar Saudiyya ya yi sanadiyyar halakar mutane akalla 13 tare da jikkatan wasu da dama.
-
Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Irakawa Kimanin 30 Tare Da Jikkata Fiye 40
May 11, 2016 05:52Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a unguwar Sadar da ke gefen birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, inda ta lashe rayukan mutane kimanin 30 tare da jikkata wasu fiye da 40 na daban.
-
Gwamnatin Bangladesh Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Jagoran Babbar Jam'iyyar Islama Ta Kasar
May 11, 2016 01:02Rahotanni daga kasar Bangalesh sun bayyana cewar an zartar da hukuncin kisa da aka yanke wa jagoran jam'iyyar Musulunci mafi girma a kasar bisa laifin da aka same shi ya aikata a lokacin yakin fafutukan neman 'yancin kasar daga Pakistan a 1971.
-
Sama Da Mutane Miliyan 40 Suke Gudun Hijira Sakamakon Yakukuwa A Duniya
May 11, 2016 01:00Cibiyar kasa da kasa mai sanya ido kan 'yan gudun hijirar da yakukuwa da rikice-rikice suka tarwatsa su ta bayyana cewa ya zuwa karshen shekaran bara ta 2015 adadin irin wadannan mutanen ya kai miliyan 40.8 a duk fadin duniya.