-
Sojojin Yamen Sun Samu Nasarar Harbo Jiragen Saman Leken Asirin Rundunar Kawancen Saudiyya
Oct 10, 2018 15:15Rundunar sojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun yi nasarar harbo jiragen saman leken asirin rundunar kawancen Saudiyya guda biyu a lardin Jizan da ke kudancin kasar Saudiyya.
-
Janar Qasim Solemani Ya Aike Da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Shahid Mughniyya
Oct 10, 2018 07:42Kwamandan dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran, Manjo Janar Qasim Solemani ya aike da sakon ta'aziyyarsa ga Sayyid Hasan Nasrullah, shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon dangane da rasuwar mahaifiyar tsohon kwamandan dakarun kungiyar Hizbullah, shahid Emad Mughniyyah, Hajiya Amina Salamah.
-
Labanon : 'Yan Gudun Hijirar Siriya Za Su Koma Gida
Oct 10, 2018 02:14Labanon ta ce adadin 'yan gudun hijirar Siriya da za su koma gida ya zuwa karshen shekarar nan ya kai 100,000.
-
Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Dan Takara A Afganistan
Oct 10, 2018 02:12Rahotanni daga Afganistan na cewa wani harin kunar bakin wake ya yi ajalin mutum 8, da kuma raunana wasu 11, a wani ofishin dan takara zaben 'yan majalisar dokoki a garin Lashkar Gah dake yankin Helmand a kudancin kasar.
-
Jiragen Kawancen Saudiya Sun Kahe Yamaniyawa 5
Oct 09, 2018 15:40A wani Sabon Harin ta'addanci da jiragen kawancen saudiya suka kai lardin Jabana na jahar Hudaidai, kimanin yamaniyawa 5 ne suka yi shahada sannan wasu shida na daban suka jikkata.
-
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Yi Luguden Wuta Kan Wata Cibiyar Lafiya A Yamen
Oct 09, 2018 08:26Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan wata cibiyar lafiya a lardin Hajjah da ke yammacin kasar Yamen.
-
Yemen: An Zargi Kasar Saudiyya Da Shelanta Yakin Tattalin Arziki Akan Kasar Yemen
Oct 09, 2018 03:15Shugaban kwamitin koli na juyin juya halin kasar Yemen, ya sanar da cewa; Kasar Saudiyya da kawayenta sun shelanta wani sabon yakin na tattalin arziki akan kasar ta Yemen
-
Za'a Ci Tarar Wadanda Suka Ki Kada Kuri'arsu A Zaben Shugaban Kasar Masar Da Ya Gabata.
Oct 08, 2018 15:27Hukumar Zabe a kasar Masar ta bada sanarwan cewa tana fitar da sunayen wadanda suka cancanci kada kuri'unnsu a zaben shugaban kasa da ya gabata amma basu yi hakan sannan ta mikawa babban mai gabatar da karan kasar don dora masu tara.
-
Morocco Ta Dakatar Da Bada Visar Shiga kasar Ga Mutanen kasar Lebanon
Oct 08, 2018 15:26Bayan tuhumar da gwamnatin kasar Morocco ta yi wa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon na tallafawa kungiyar Polisario gwamnatin kasar ta bada sanarwan dakatar da visar shiga kasar ga yan kasar Lebanon.
-
Turkiya: Ana Zargin An Kashe Khashoggi A Cikin Karamin Ofishin Jakadancin Saudiyya
Oct 07, 2018 03:44Sakamakon farko na binciken da 'yan sandan kasar Turkiya suka gudanar kan bacewar fitaccen dan jaridar Saudiyya mai sukar gwamnati na nuni da cewa, an kashe shi ne a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul.