Mutane 12 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Bomb A Kasar Philiphines
Rahotanni daga kasar Philippine sun bayyana cewa alal akalla mutane 12 sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka sakamakon fashewar wani bomb da aka dana a garin Davao, mahaifar shugaban kasar Rodrigo Duterte a jiya Juma'a.
Kakakin karamar hukumar Davao din Catherine Dela Rey ta shaida wa manema labarai abkuwar fashewar inda ta ce mutane da dama sun rasa rayukansu da kuma samun raunuka, sai dai ta ce har ya zuwa lokacin ba a tantance musabbabin fashewar ba da ta faru a kusa da wani waje da ke kusa da yankin da ke dauke da wasu manyan otel otel na birnin inda mafi yawan 'yan yawon shakatawa suke zama.
Kafin hakan ma dai kakakin fadar shugaban kasar Ernesto Abella ya tabbatar da faruwar fashewar bomb din a garin na Davao da ke kimanin kilomita 1500 daga babban birnin kasar Manilla.
Duk da cewa babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin amma wasu majiyoyi dai suna nuna yatsar zargi ga masu fataucin muggan kwayoyi wadanda shugaba Rodrigo Duterte yake fada da su tun da ya hau karagar mulki, sannan wasu majiyoyin kuma sun ce a baya sun sha masa barazanar kai masa hari. An ce shugaban dai yana garin a lokacin da wannan fashewar ta faru.
A baya ma dai garin Davao din ya fuskanci hare-haren 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Abu Sayyaf.