Alhazai Sun Fara Shirye-Shiryen Fara Aikin Hajji A Gobe Asabar
Miliyoyin alhazai da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya na shirin fara aiwatar da aikin hajji na bana a gobe Asabar a garin Makka ranar da ake kiransa da 'ranar tarwiyya' duk kuwa da raguwar yawan alhazan da aka samu a bana.
Mahukuntan Saudiyyan dai sun ce adadin maniyyatan na bana ya kai mutane miliyan biyu da dubu dari biyu da saba'in, inda tuni garin Makka dai ya cika makil da mahajjatan wadanda suke shirin fara aikin hajjin a gobe Asabar.
Rahotanni dai sun ce duk da tsananin zafin rana da ake fama da shi da aka ce ya kai maki 45 na ma'aunin zafi din maniyyatan na bana suna ta shirye shiryen sauke farali cikin matsanancin yanayin tsaro da mahukutan Saudiyyan suka dauka da sunan ba da kariya ga maniyyatan.
Za a gudanar da aikin hajjin na bana ne ba tare da mahajjatan kasar Iran ba sakamakon sharuddan da mahukuntan Saudiyyan suka sanya lamarin da ya sanya jami'an Iran cikin damuwar lafiya da tsaron mahajjatan kasar don gudun faruwar abin da ya faru a yayin hajjin bara inda daruruwan mahajjatan kasar Iran din suka rasa rayukansu a turmutsutsin da ya faru a Mina lamarin da har ya zuwa yanzu mahukutan Iran da ma wani adadi mai yawa na al'ummomi da 'yan siyasa da masanan kasashen musulmi daban-daban suke dora alhakin faruwar hakan a kan mahukuntan Saudiyyan.
Dubun dubatan maniyya da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya ne suka rasa rayukansu a yayin wannan turmutsutsin da ya faru a Mina a ranar babbar salla.