Musulmai Dake Aikin Hajji Na Tsayuwar Arfa
Yau Lahadi ce tara ga watan Zul-Hijja al'ummar musulmi da su ka samu sukunin yin aikin hajjin bana ke tsayuwar Arfa, a filin Arfa da ke wajen birnin Makkah.
Tun a jiya Asabar ne dai maniyata aikin hajjin na bana sanye da harami su ka fara fita zuwa Muna inda za su share akasarin yau su na gudanar da ibada a filin na Arfa wanda shi ne kololuwa na aikin hajji.
Hukumomin Saudiyya dai sun ce kimanin mutane miliyan daya da dari takwas da hamsin da biyar ne za su gudanar da aikin hajjin na bana.
A wannan karo dai hukumomin Saudiyya sun ce sun dau kwararen matakai domin kaucewa irin matsalolin da aka fuskanta a bara, wanda ya hadassa rasuwar dubban mahajjata a wajen turmutsutsun da aka samu wajen jifan shaidan.