Ana ci gaba da ceton 'yan hijra a ruwan Bahrum
Kungiyar Agaji ta sanar da ceto 'yan gudun hijra kimanin 700 a ruwan Meditaraniya
A wata sanarwa da ta fitar a wannan Lahadi, Kungiyar Agaji ta kasa da kasa ta ce kimanin bakin haure 700 ne ta ceto daga hallaka a yayin da suka cikin kananen jiragen ruwa marassa inganci da suka fito daga kasar Libiya a gudancin Ruwan Meditaraniya, daga cikin su a kwai Mata da yara kanana da ba su fice watani uku zuwa hudu a Duniya ba.
Sanarwar ta ce tuni wadanda ake ceton aka basu taimakon farko inda aka diba lafiyar su tare da basu abinci gami da kayan sawa da na shinfida.
A cikin wani sabon rahoto da hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta fitar, daga farkon wannan shekara ta 2016 zuwa yanzu kimanin bakin haure dubu 105 suka isa tsibirin kasar Italiya, kuma akasarinsu sun biyo ne daga kasar Libiya, baya ga haka dubu biyu da 726 sun hallaka a cikin ruwa kafin su kai ga tsibirin kasar ta Italiya.