Rasha ta fara gudanar da aikin Agaji a Halab na Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10951-rasha_ta_fara_gudanar_da_aikin_agaji_a_halab_na_siriya
Ministan Harakokin wajen Rasha ya sanar da cewa bayan yarjejjeniyar tsagaita wuta na maku guda na guda, ba tare da bata lokaci ba, jami'an Agajin kasar za su fara gudanar da aiyukan su a garin Halab.
(last modified 2018-08-22T06:58:55+00:00 )
Sep 13, 2016 00:43 UTC
  • Rasha ta fara gudanar da aikin Agaji a Halab na Siriya

Ministan Harakokin wajen Rasha ya sanar da cewa bayan yarjejjeniyar tsagaita wuta na maku guda na guda, ba tare da bata lokaci ba, jami'an Agajin kasar za su fara gudanar da aiyukan su a garin Halab.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin, Mista Lavrov ya ce ba tare da bata lokacin ba za su fara kai kayan agaji ta hanyar Kaslito zuwa cikin Halab.

Ministan harakokin wajen Rashan ya kara da cewa ganin yadda Amurka ke da karfin fada a jini a tsakanin 'yan adawa masu sassaucin ra'ayi, sun bukaci magabatan siriyan da su amince da yarjejjeniyar sulhu na maku guda domin bayar wa Al'umma gudanar da shagulgulan babbar salla tare kuma da shigar da kayan agaji cikin yankunan da rikici ya yi tsanani kamar Halab da Alepo.

Ma'aikatar Harakokin wajen Rashan ta bayyana damuwar ta na rashin mutunta yarjejjeniyar tsagaita wutan daga wasu bangarori na kungiyoyi masu dauke da makamai, inda ta jan kunan kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Ahraru Sham da kadda su kuskura su karya wannan yarjejjeniya.

Bisa yarjejjeniyar da aka cimma tsakanin magatan Amurka da Rasha, tun daga safiyar babbar salla ne, yarjejjeniyar tsagaita wutar ta fara aiki har zuwa maku guda.Duniya dai na fatan wannan yarjejjeniya ta dore, kuma ta zamanto ita ce sanadiyar karshen yakin da kasar ta kwashe kusan shekaru biyar tana fama da shi.