MDD / Libya : Bakin Haure 235,000 Ke Zawarcin Shiga Italiya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11071-mdd_libya_bakin_haure_235_000_ke_zawarcin_shiga_italiya
MDD, ta yi gargadin cewa bakin haure kimanin 235,000 dake Libya yanzu haka ke shirye domin kwarara zuwa Italiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 15, 2016 05:06 UTC
  • MDD / Libya : Bakin Haure 235,000 Ke Zawarcin Shiga Italiya

MDD, ta yi gargadin cewa bakin haure kimanin 235,000 dake Libya yanzu haka ke shirye domin kwarara zuwa Italiya.

Wakilin MDD a wannan kasar ta Libya, Martin Kobler ya fada a wata hida da jaridar ''Stampa'' cewa suna da jaerin sunayen bakin haure 235,000 da yanzu suke jiran lokaci kawai domin tafiya Italiya, kuma babu abunda zai katse masu hamzari akan wannan anniya.

Don haka a cewarsa karfafa matakan tsaro shi ne kawai yanzu mafi mahimmanci a yanzu, inda a cewarsa kuma idan muna da rundina mai karfi da hadin kai zamu kawar da duk wata barazanar ta'adanci da kuma safara mutane.

Kafin hakan dai wasu al'kalumma da ma'aikatar cikin gidan Italiya ta fitar a Jiya Laraba na nuna cewa yawan bakin hauren da suka shiga kasar ta tekum bahar Rum tun daga farkon wannan shekara ya kai 128,397, adadin daya karu da kashi 5,15% idan aka kwatamta dana bara warhaka.