Kungiyar Tarayyar Turai ta sabunta takunkumin da ta Kakabawa Rasha
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11086-kungiyar_tarayyar_turai_ta_sabunta_takunkumin_da_ta_kakabawa_rasha
Kungiyar tarayyar Turai ta sabunta takunkumin da ta kakabawa wasu kamfanoni da Mutanan kasar da Ukrene
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 15, 2016 11:53 UTC
  • Kungiyar Tarayyar Turai ta sabunta takunkumin da ta Kakabawa Rasha

Kungiyar tarayyar Turai ta sabunta takunkumin da ta kakabawa wasu kamfanoni da Mutanan kasar da Ukrene

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a yau Alkhamis Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da sabinta takunkumin da ta kakabawa kimanin Mutane 200 na kasashen Rasha da Ukrene wadanda take zarki na barazanar mamaye kasar Ukrene har zuwa watani shida masu zuwa wato har zuwa 15 ga watan Maris na shekara 2017 mai kamawa.

Majalisar Kungiyar tarayar Turan ta sanar da cewa takunkumin ya shafi rufe asusun ajiya da kuma hana Mutanan shiga cikin kasashen Turai da adadin su ya kai 146 tare kuma da wasu Kamfanoni 37 gami da wani bangane na kungiyoyin siyasa, takunkumin na Tarayyar Turai ya fara ne tun daga watan Maris din shekarar 2014 .magabatan kasar Rasha sun mayar da martani dangane da takunkumin da kasar Amurka gami da kungiyar tarayyar Turai suka kakabawa 'yan kasar ta Rasha gami da wasu kamfanoni.

Rikici tsakananin kasashen Rasha,da kasar Amurka gami da kungiyar Tarayyar Turai ya samo asali ne tun bayan da Al'ummar tsibiri Karima na kasar Ukrene suka jefa kuri'a na ballewa daga kasar Ukrene din tare da hadewa da kasar Rasha.