Jam’iyyar Putin Tayi Rinjaye A Zaben 'Yan Majalisa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11233-jam’iyyar_putin_tayi_rinjaye_a_zaben_'yan_majalisa
Rahotanni daga Rasha na cewa Jam’iyyar shugaban kasar Vladimir Putin na sahun gaba da gagarimin rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka kada kuri'arsa jiya lahadi.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Sep 19, 2016 01:04 UTC
  • Jam’iyyar Putin Tayi Rinjaye A Zaben 'Yan Majalisa

Rahotanni daga Rasha na cewa Jam’iyyar shugaban kasar Vladimir Putin na sahun gaba da gagarimin rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka kada kuri'arsa jiya lahadi.

Bayanai sun nuna cewa kawo yanzu  jam'iyyar ta samu kashi 54.3 % a cikin kashi 90% na yawan kuri'un da aka kada, wanda kuma hakan zai bata damar samun rinjaye mai yawa a majalisar dokokin kasar.

A hasashen da akayi jam'iyyar ta United Russia zata iya samun akalla kujeru 338 cikin 450 da majalisar ta Duma ta kunsa, sai kuma wasu jam'iyyu biyu wanda ke dasawa da gwamnatin kasar dake biyo baya.

Jam'iyyun dake biyo bayan jam'iyyar ta shugaba Putin su ne jam'iyyar 'yan kwaminis da kuma ta nationalists LDPR.