Martanin Shugaban Gwamnatin Jamus bayan fitar da sakamakon zabe na Berlin
(last modified Mon, 19 Sep 2016 17:44:28 GMT )
Sep 19, 2016 17:44 UTC
  • Martanin Shugaban Gwamnatin Jamus bayan fitar da sakamakon zabe na Berlin

Shugaban Gwamnatin Jamus ta daukin kayin da Jam'iyyarta ta sha a birnin Berlin

A wannan Litinin Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ta dauki alhakin mummunan kayen da jam'iyyarta ta CDU ta sha a zaben majalisar dokoki a Berlin. Sai dai kuma ta dage cewa ba za ta sauya manufarta kan yan gudun hijira ba musaman ma musulmi.sannan ta kara da cewa kamata ya yi ta bada kulawa ta musaman ga siyasar ta na taimakon 'yan gudun hijra.

Merkel ta ce sakamakon zaben da aka yi a karshen mako abu ne mai matukar takaici da rashin jin dadi ga Jam'iyyar CDU. dalilin hakan kuwa shine ba'a yi cikakken bayani ga jama'a da za su fahimta game da manufarta ta karbar yan gudun hijira ba.

Merkel ta yi alkawarin cewar za ta yi bakin kokari na magance damuwar jama'a akan manufofinta kan yan gudun hijira.

A jiya Lahadi ne aka gudanar da zaben 'yan Majalisun na birnin Berlin, inda jam'iyyar  SPD ta samu kashi 21.6 a zaben, yayin da Jam'iyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta zo ta biyu  da kashi 18 cikin dari na kuri'un da aka kada, sai kuma  jami'yyar AFD ta masu kyamar baki ta zo ta uku  da kashi 14.2 cikin dari.