Fidel Castro Ya Jinjinawa Tsayin Dakan Al'ummar Iran Wajen Tinkarar Takunkumi
(last modified Tue, 20 Sep 2016 09:22:31 GMT )
Sep 20, 2016 09:22 UTC
  • Fidel Castro Ya Jinjinawa Tsayin Dakan Al'ummar Iran Wajen Tinkarar Takunkumi

Tsohon shugaban kasar Cuba kuma jagoran juyin juya halin kasar Fidel Castro, ya jinjinawa irin tsayin dakan da al'ummar Iran suka yi wajen tinkara da kuma fada da takunkumin karya tattalin arziki na zalunci da aka sanya wa kasar.

Shugaba Castro ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani wanda ya kai ziyarar aiki kasar ta Cuba inda ya ce: Tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran ya sanar da goyon bayansa ga wannan juyi da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya jagoranta.

Mr. Castro ya  kara da cewa tsayin dakan da al'ummar Iran suka yi wajen tinkarar takunkumin da aka sanya wa kasar wani abin jinjinawa ne wanda kuma yake nuni da irin fadaka da kyawawan al'adu da al'ummar Iran din suke da shi. Har ila  yau Mr. Castro ya ce ya saurari jawabin da shugaba Ruhanin yayi a wajen taron kungiyar 'yan ba ruwanmu a kasar Venezuela wanda yace hakan wani lamari ne mai karfafa gwiwa ga al'ummomin yankin Latin Amurka.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana farin cikinsa dangane da ziyarar da ya kawo kasar Cuban da kuma ganawar da yayi da shugaba Castro din, kamar yadda kuma ya ce al'ummar Iran dai duk da irin matsin lamba da takunkumi na zalunci da aka sanya mata amma ta sami nasarori masu yawa a fagen tattalin arziki.

A safiyar yau Talata ce dai shugaban kasar Iran din ya isa kasar ta Cuba don amsa gayyatar da takwararsa na kasar Raul Castro yayi masa.