Saudiyya Ta Zabge Albashin Ma'aikatan Kasar Sakamakon Matsalar Tattalin Arziki
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11623-saudiyya_ta_zabge_albashin_ma'aikatan_kasar_sakamakon_matsalar_tattalin_arziki
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da wasu sabbin matakai na rage albashin ministoci da wasu hakkoki na ma'aikatan gwamnatin kasar da kashi 20 cikin dari don cike gibin kasafin kudin da take fuskanta biyo bayan faduwar farashin mai da kuma kudaden da ta kashe wajen sayo makamai lamarin da ya sanya tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.
(last modified 2018-08-22T06:58:59+00:00 )
Sep 27, 2016 02:20 UTC
  • Saudiyya Ta Zabge Albashin Ma'aikatan Kasar Sakamakon Matsalar Tattalin Arziki

Gwamnatin Saudiyya ta sanar da wasu sabbin matakai na rage albashin ministoci da wasu hakkoki na ma'aikatan gwamnatin kasar da kashi 20 cikin dari don cike gibin kasafin kudin da take fuskanta biyo bayan faduwar farashin mai da kuma kudaden da ta kashe wajen sayo makamai lamarin da ya sanya tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.

Gidan talabijin din Al-Ekhbariyya na kasar Saudiyyan ne ya sanar da hakan yayin da yake ishara da taron da 'yan majalisar ministocin kasar suka gudanar  karkashin jagorancin sarki Salman inda aka sanar da shirin gwamnatin na dakatar da wasu hakkokin da kyaututtuka da ake ba wa jami'ai da ma'aikatan gwamnati na kasar.

A cikin wani rahoto da gidan talabijin din ya watsa daga baya an yi karin haske dangane da wannan mataki da aka dauka da suka hada da rage albashin ministocin kasar da kashi 20 cikin dari, sannan su kuma 'yan majalisar shura na kasar za a rage musu albashin na su da kashi 15 cikin dari, bugu da kari kan rage wasu hakkoki da ma'aikatan gwamnatin kasar suke da su a da.

Wannan sabon matakin dai yana daga cikin matakan da gwamnatin Saudiyyan take dauka don rage irin kashe kudin da ake yi a kasar sakamakon matsalar tattalin arziki da gwamnatin take fuskanta sakamakon faduwar farashin man fetur bugu da kai kuma kan irin makudan kudaden da Saudiyyan  take kashewa wajen sayen makamai a hare-haren da take ci gaba da kai wa kasar Yemen da kuma wadanda take  ba wa 'yan ta'addan da suke yaki a kasaashen Siriya da Iraki.