Rasha ta mayar da martani kan barazanar Amurka
Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta mayar da martani kan barazanar da magabatan Amurka su ka yi na yanke alaka da kasar a kan warware rikicin kasar Siriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Laraba, Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta bayyana cewa a hirar da Sergei Lavrov Ministan harakokin wajen kasar ya yi ta hanyar Tarho da takwaransa na kasar Amurka Jean Kery babu batun yanke alaka tsakanin kasashen biyu kan batun warware rikicin kasar Siriya, saidai Lavrov ya tunatar da kery cewa wasu daga cikin kungiyoyin 'yan adawa da ake kira masu sassaucin ra'ayi ba su amince da yarjejjeniyar tsagaita wuta da buranan Masco da Washinton suka cimma ba,sannan sun bi sahun kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatu-Nusra.
Har ila yau rahoton ya ce jami'an Diplomasiyar na kasashen Rasha da Amurka sun tattaunawa kan irin matakan da ya kamata a dauka da kuma zai yi tasiri kan makomar garin Halab bisa kan turbar yarjejjeniyar tsagaita wuta.
A Jiya Laraba ce Ma'aikatar Harakokin wajen Amurka ta sanar da cewa Kery ya shaidawa Lavrov cewa Amurka ta fara shirye-shiryen dakatar da alakar dake tsakanita da Rashe matukar dai ba ta dakatar da hare-haren da take kaiwa birnin Halab ko kuma Allepo ta sama ba.
Amurka da kawanta na kara matsin lamba ga Kasar Rasha domin ta dakatar da hare-haren da take kaiwa 'yan ta'adda a birnin Allepo na kasar Siriya.