Kai Kara Saudiyya, Zai Haifar Da Mummunan Sakamako Ga Amurka
Ma'aikatar harkokin wajen Saudiya ta fitar da wata sanarwa da ke gargadi cewa, kudurin da majalisar dokokin Amurka ta zartas wanda ke nuna goyon bayan iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata sakamakon harin ranar 11 ga watan Satumba da su kai karar gwamnatin Saudiya, zai haifar da mummunan sakamako ga Amurka.
A ranar Laraba data gabata ce, majalisu biyu na Amurka suka hau kujerar naki akan bukatar shugaba Barack Obama na kin kai karar gwamnatin Saudiya.
Shi dai Obama ba ya goyon bayan iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata su kai karar gwamnatin Saudiya.
Sai dai wasu iyalan wadanda suka mutu sakamakon harin na ranar 11 ga watan satumban 2001 suna bukatar Saudiyya ta dauki alhakin abunda ya faru, kasancewar kungiyar 'yan ta'addan AL'Qaeda data kai harin tana samun kudadenta ne daga gwamnatin ta Saudiyya.