Facebook Ya Kirkiro Da Shafin Fullanci
Shafin sada zumunta na Facebook ya kirkiro da shafin fullanci, sakamakon yadda fillani ke amfani da shafin kamar sauran kabilu a duniya.
Facebook ya kaddamar da tsarin ne a wannan Juma'a 30 ga watan Satumba 2016, inda yanzu fullanci ya kasance harshe na 101 da yake amfani da shi.
Yanzu fullanci ya samu shiga sahun harsunan Afrika a Facebook bayan harshen hausa, Somalia da Swahili da Afrikaans da Kinawarwanda.
Fullanci harshe ne da shi ma yawancin mutanen kasashen yammacin Afrika ke amfani da shi musamman a kasashen Najeriya da Nijar da Mali.
Shafin facebbok dai na samun karbuwa sosai a duniya, idan aka kwatamta da shekara 2008 inda yake aiki da harsunan Ingilishi da Spanish.
Kusan mutane miliyan 84 ke amfani da shafin sada zumunta na facebook a yankin Afrika dake kudu da hamadar sahara.