Rasha ta galgadin Amurka kan hari ga Sojojin Siriya
Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta galgadi Amurka da kadda ta kuskura ta kai hari kan Sojojin Siriya
Tashar Telbijin din Rusiya Alyaum ta nakalto Ma'aikatar harakokin wajen Rasha na cewa, matukar dai Amurka ta kuskure ta kai hari kan Sojojin Siriya da Birnin Damuscus to shakka babu komai na iya canzawa kuma hakan na iya janyo canji mai tayar da hankali a gabas ta tsakiya.
Bayyanin da Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta fitar a wannan Assabar, ta ce matukar dai aka canza Gwamnati a Siriya, to kasar za ta kasance sansani 'yan ta'adda domin haka babu yadda za mu amnice hakan ya kasance.
Yarjejjeniyar tsagaita wuta a kasar Siriyan da magabatan Masco da Washinton suka cimma ta kawo karshe ne tun bayan da Jiragen yakin Amurka suka kai mumunan hari kan Sojojin Siriya da kuma harin da aka kai kan tawagar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya.
A cikin 'yan kwanakin nan Amurka da kawayenta na ci gaba da kara matsin lamba kan kasar Rasha a kan ta dakatar da hare-haren da take kaiwa kan 'yan ta'adda a birnin Halab ko kuma Allepo.
Tun daga shekara 2011, kasar ta Siriya ta fada cikin yaki bayan da kasar Saudiya tare kasar Amurka da kawayenta suka ingiza wasu kasar da su yi shugaba Asad tawaye, bayan da ba su nasara ba sai suka fara tattaro Matasa daga kasashen Duniya suka basu horon ta'addanci da sunan jihadi sannan kuma suke tura su cikin kasar ta hanyar kasar Turkiya.