Rasha Ta Jaddada Wajabcin Kawo Karshen 'Yan Ta'adda A Kasar Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12187-rasha_ta_jaddada_wajabcin_kawo_karshen_'yan_ta'adda_a_kasar_siriya
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya jaddada cewa; Dole ne a dauki matakin kawo karshen 'yan ta'adda a Siriya domin al'ummar kasar su zauna lafiya.
(last modified 2018-08-22T06:59:03+00:00 )
Oct 09, 2016 02:49 UTC
  • Rasha Ta Jaddada Wajabcin Kawo Karshen 'Yan Ta'adda A Kasar Siriya

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya jaddada cewa; Dole ne a dauki matakin kawo karshen 'yan ta'adda a Siriya domin al'ummar kasar su zauna lafiya.

A zantawarsa da takwaransa na kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ta hanyar wayar tarho; Ministan harkokin wajen kasar Rasha Seigei Lavrov ya fayyace irin halin tsaka mai wuya da kasar Siriya take ciki sakamakon yadda 'yan ta'adda suke ci gaba da yin kafar ungulu ga yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma musamman a garin Halab.

Sergei Lavrov ya kuma jaddada wajabcin karfafa shirin dakatar da bude wuta a yankunan da ake tsananin bukatar aikewa da kayayyakin jin kai a kasar ta Siriya, amma a bangare guda kuma dole ne a ci gaba da murkushe 'yan ta'adda a kasar.

A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana shirin kasarsa na hada kai da tawagar Majalisar Dinkin Duniya a fagen isar da kayayyakin jin kai ga al'ummar yankunan garin Halab da suke cikin mawuyacin hali.