Jamus : An Cafke Mutumin Dake Shirin Kai Harin Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12238-jamus_an_cafke_mutumin_dake_shirin_kai_harin_ta'addanci
'Yan sanda a Jamus sun sanar da cafke matashin nan da asalin kasar Siriya da aka kwashe wunin jiya ana farautarsa bisa zargin shirin kai harin ta'addanci a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:03+00:00 )
Oct 10, 2016 02:22 UTC
  • Jamus : An Cafke Mutumin Dake Shirin Kai Harin Ta'addanci

'Yan sanda a Jamus sun sanar da cafke matashin nan da asalin kasar Siriya da aka kwashe wunin jiya ana farautarsa bisa zargin shirin kai harin ta'addanci a kasar.

Wata sanarwa da hukumar 'yan sanda kasar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce tayi nasara cafke mutumin mai suna Jaber Albakr a cikin daren jiya a yankin Leipzig.

An dai cafke shi ne a gidan wasu Siriyawa inda ya buya.

A ranar Asabar data gabata dai 'yan sanda sun sanar da gano wasu ababe masu fashewa a gidan Albakr din dake yankin Chemnitz dake nisan kilomita 260 a kudancin Berlin.

Ana dai zargin mutimin dan shekaru 22 da yin mu'amula da kungiyar 'yan ta'addan IS ta hanyar Internet.