Farashin Man Fetur Ya Tashi A Kasuwar Hada-Hadar Man
Rahotanni sun bayyana cewar an samu tashin farashin man fetur a kasuwar duniya ban sanarwar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayi na cewa kasarsa a shirye take ta goyi bayan kokarin da kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur take yi na takaita irin man da ake fitarwa a kowace rana.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya ce a cinikin da aka yi a jiya a kasuwar mai din ta Amurka farashin man ya tashi da dala 1 da centi 54 lamarin da ya kai farashin mai din zuwa dala 51.35 a kan kowace gangan gurbataccen man lamarin da aka ce shi ne karon farko da farashin mai din ya kai haka a wannan shekarar ta 2016.
Masana harkokin mai din dai sun bayyana cewar tashin farashin mai din ya biyo bayan kalaman shugaban kasar Rashan a wajen taron kasa da kasa kan makamashi da aka gudanarda shi a kasar Turkiyya.
A ranar 28 ga watan Satumbar da ya gabata ne a membobin kungiyar ta OPEC suka amince da rage irin adadin man fetur din da suke fitarwa a kowace rana.