An kai hari kan ofishin jakadancin Rasha a Siriya
Wasu 'yan ta'adda sun harba iguwa a kan Ofishin jakadancin Rasha dake birnin Damuscus na kasar Siriya
A wata sanarwa da Ma'aikatar harakokin wajen kasar Rasha ta fitar a wannan Alkhamis, ta ce wasu 'yan ta'adda a Siriya sun kai harin ta'addanci ta hanyar halba iguwa a kan ginin ofishin jakadancin kasar dake birnin Damuscus, lamarin da ya yi sanadiyar lalata wani bangare na ofishin wakilin siyasar kasar.
Bayan yin alawadai da wannan ta'addanci, Ma'aikatar harakokin wajen ta Rasha ta ja kunnan kasashen dake goyon bayan 'yan ta'addan a Siriya, an bayyana cewa an halbo iguwa din ne daga birnin Jubair na gefen birnin Damuscus inda ke kalkashin ikon 'yan ta'adda na Jabhatu Nusra.
A makon da ya gabata ma, Ofishin jakadancin na Rasha da ke birnin Damuscus ya fuskanci irin wannan hari na iguwa da ya fado a harabar ofishin da kuma kusa da gidajen Ma'aikatan sa.