An kori Alkalan Kotun Soja 109 a Turkiya
(last modified Fri, 14 Oct 2016 11:02:12 GMT )
Oct 14, 2016 11:02 UTC
  • An kori Alkalan Kotun Soja 109 a Turkiya

Alkalan kotun Soja 109 aka kora daga cikin Sojojin Turkiya saboda zarkin su da alaka da kungiyar Fethullah Gülen

Kafafen yada labarai na kasar turkiya sun watsa kudirin Ma'aikatar tsaron kasar dangane da korar wadannan sojoji 109 da aka kora a wannan Juma'a, tare da bayyana matakin da kwamitin Alkalan sojan kasar ya dauka, inda dukkanin manbobin kwamitin suka kada kuri'ar korar wadanan sojoji.daga cikin wadanda wannan kora ta shafa harda Janar Khairuddin Kaldyrmajy tsohon mashawarci a kotun Dakarun tsaron kasar.

kafin yunkurin juyin milkin da bai ci nasara ba a kasar, Rundunar tsaron Turkiya na da Alkali Sojoji 468, to amma bayan wannan yunkurin juyin milki, adadin ya ragu zuwa 209 sannan kuma a halin da ake ciki a kwai wasu 10  da ake ci gaba da bincike a kansu.