Girgiza Kasa Mai Karfi Ta Abkawa Italiya
Hukumar bayar da agaji a Italiya ta sanar da cewa an samu mumunar barna a girgiza kasa mai karfin maki 6.5 ata abkawa kasar yau Lahadi.
Wannan dai ita girgiza kasa mafi karfi da kasar ta fuskanta tun bayan shekara 1980.
Girgiza kasa dai ta auku ne a tsakiyar kasar a kusa da birbin Norcia, inda ta rusa manya-manyan gine-gine.
Har kawo yanzu dai ba'a samu bayyanai akan ko girgiza kasar ta kashe ba, amman an ce akwai mutane kimanin ashirin da suka raunana.
Wannan girgizar kasar ta abku ne wata biyu bayan wata makamanciyarta ta abkawa kasar, inda ta kashe kusan mutum 300 sannan ta lalata garuruwa da dama.
Marabin da a fuskanci irin girgiza kasa mai karfi kamar haka tun bayan mai karfin maki 6.9 data aukawa kasar a shekara 1980 inda mutane kimanin 3,000 suka rasa rayukansu.