Rasha za ta fara kai farmaki kan 'yan ta'adda a Siriya
Wata majiya a Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce nan ba da jimawa ba Dakarun tsaron kasar za su fara kai farmaki kan 'yan ta'adda a garin Alepo
Wata majiya a Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar a wannan Laraba cewa ba da jimawa ba Dakarun ruwan Rasha dake tekum Meditereniya za ta fara kai farmaki kan 'yan ta'addar dake samun goyon bayan kasashen yamma da wasu kasashen Larabawa a birnin Halab ko kuma Alepo.
Majiyar ta ce harin zai kasance a lokaci guda, jiragen ruwan Rashan dake tekum Meditereniya da jiragen yakin kasar dake jibke a sansanin Sojan Rasha dake kasar Siriya za su yi amfani da sabin makaman zamani wajen rusa duk wani sansani na 'yan ta'adda dake birnin na Halab.
Kafin kai wannan farmaki, Majiyar ta ce za ayi amfani da na'urorin zamani da suka hada da jirage marassa matuka wajen gano wuraren taruwar 'yan ta'addar a birnin na Alepo.