Donald Trump ya tattauna da Putin ta hanyar waya.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13906-donald_trump_ya_tattauna_da_putin_ta_hanyar_waya.
Fadar Shugaban kasar Rasha ta sanar da cewa Shugaba Viladimin Putin ya tattauna da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ta wayar Talho a daren jiya Litinin.
(last modified 2018-08-22T06:59:14+00:00 )
Nov 15, 2016 02:23 UTC
  • Donald Trump ya tattauna da Putin ta hanyar waya.

Fadar Shugaban kasar Rasha ta sanar da cewa Shugaba Viladimin Putin ya tattauna da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ta wayar Talho a daren jiya Litinin.

Jaridar Alyaumu sabi'i ta kasar Rasha ta habarta cewa a daren jiya Litinin zababben Shugaban kasar Amurka tare da takwarsa na Rasha sun tattauna kan rikicin kasar Siriya inda suka tabbatar da cewa za su ci gaba da wannan tattaunawa domin magance wannan rikici da aka kwashe sama da shekaru biyar a cikin sa

Sanarwar ta kara da cewa Shugabanin sun tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za su gana da juna domin ci gaba da kokari wajen kawo karshen ta'addanci a Duniya, a baya dai Shugaba Putin na kasar Rasha ya sanar da cewa Birnin Masco a shirye yake ya yi aiki tare da sabuwar Gwamnati Amurka bisa mutunta juna ba tare da yin katsa landan a harakokin cikin gida wata kasa daga ciki ba.

Har ila yau sanarwa ta ce magabatan biyu sun tabbatar da fadada alaka na aiki tare a tsakanin su, da kuma ci gaba da tattaunawa dangane da abinda ya shafi bangarori daban-daban tare da medo alakar kasashen kamar yadda take a baya.