Boko Haram Ta Sake Kashe Wani Kwamandan Sojin Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13942-boko_haram_ta_sake_kashe_wani_kwamandan_sojin_najeriya
Rahotanni dake cin karo da juna a Najeriya na cewa Wa kungiyar Boko Haram ta sake hallaka wani Laftanar Kanal na rundunar sojin kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 15, 2016 14:53 UTC
  • Boko Haram Ta Sake Kashe Wani Kwamandan Sojin Najeriya

Rahotanni dake cin karo da juna a Najeriya na cewa Wa kungiyar Boko Haram ta sake hallaka wani Laftanar Kanal na rundunar sojin kasar.

Laftanar Kanal B.U. Umar, da ke shugabantar bataliya ta 114 ta rundunar sojin Najeriya tare da wasu sojoji, sun gamu da kwanton Bauna ne daga mayakan Boko Haram yayin da suke kan hanyar zuwa garin Piridang na jihar Adamawa daga garin Bita na jihar Borno.

Kamar yadda wasu jaridu a Najeriya suka rawaito, an ce daga fari motar da Laftanar Kanal B.U. Umar yake ciki ta taka nakiya, sai dai babu abin da ya same shi.

Bayan fitowarsa ne daga motar, mayakan na Boko Haram suka bude masa wuta, nan take kuma ya rasa ransa tare da wasu sojoji kamar yadda wata majiya soji ta shaidawa jaridar PREMIUM TIMES.

Wannan dai na zuwa kwanaki kadan bayan da kungiyar ta B.H ta kashe wani hafsan na sojin Najeriya, Laftana Kanar Muhammed Abu-Ali, da dakarunsa a wani harin kwantan-bauna.