Tarayyar Turai Na Cikin Rudani Sakamakon Zaben Trump A Amurka
A ranar Talata da ta gabata ce ministocin harkokin waje da na tsaro na kasashen kungiyar tarayyar turai suka gudanar da wani zaman gaggawa a birnin Brussels na kasar Belgium, inda suka tattauna muhimman batutuwa a suka shafi batun ayyukan tsaro da makomar alaka ta wannan fuska tsakaninsu da kasar Amurka.
Wannan zama dai ya zo ne sakamakon irin furucin da ke fitowa daga bakin zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump, a kan yiwuwar kawo karshen yarjejeniyar kariya ta tsaro da Amurka ke baiwa kasashen turai, wadda aka rattaba hannu a kanta a ranar 4 ga watan Yunin shekara ta 1947, wanda kuma wannan yarjejeniya ita ce mafi tasiri a cikin dukkanin yarjeniyoyi da suka hada kasashen da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO daga nahiyar turai da kuma kasar ta Amurka, wanda hakan ne ma yasa kasashen tarayyar turan suke ganin cewa kawo karshen wannan yarjejeniya yana a matsayin kawo karshen ayyukan Amurka a cikin NATO.
Wannan ne ma ya sanya babbar jami'a mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta bayyana a wajen taron cewa na birnin Brussels cewa, babbar manufar taron ita ce samar da wani tsari na tsaro mai zaman kansa na kungiyar tarayyar turai zalla, ba tare da ambaton Amurka ko wasu kasashen da ke kawance da turai a cikin NATO ba.
Wannan dai shi ne karon farko da ministocin harkokin waje da na tsaron kungiyar tarayyar turai suka hadu kan wannan batu sakamakon wadannan kalamai da suka fito daga bakin Donald Trump, inda suke kallon hakana matsayin wata barazana mafi girma da ke fuskantar kungiyar tarayyar turai, wanda tasirin hakan ba zai takaita kan dakushe alakar tsaro tsakaninsu da Amurka ba kawai, zai yi tasiri wajen bayar da dama ga masu tsatsauran ra'ayi a cikin manyan 'yan kasuwa na kasashen turai su iya samun isa ga kujerun shugabancin kasashen turai, kamar yadda Trump ya zo babu zato babu tsammani, kuma daga irin kalaman da suka rika fitowa daga bakunan shugabanni da manyan jami'an kasashen tarayyar turai bayan da Trump ya lashe zaben Amurka, za a iya fahimtar cewa ba su ganin hakan a matsayin wata bushara ta alkhairi ga makomar siyasarsu, musamman ma ganin cewa tun kafin zuwa Trump kungiyar tarayyar turai ta fara fuskantar matsalar wanzurta a matsayin tarayya tun bayan da Birtaniya ta fita daga cikin kungiyar, kamar yadda a halin yanzu haka wasu kasashe irin su Hungary da kuma jamhuriyar Czech suke neman bin sahun Birtaniya
Wani abu wanda ya kara daga hankulan kasashen tarayyar turan shi ne, yadda Trump ya fara yin barazanar rage ayyukan Amurka a cikin NATO musamman ma a gabashin turai, da kuma yadda ya nuna karkata ga neman sulhuntawa tare da Rasha, wanda ko shakka babun kasashen kungiyar tarayyar turai ba za su yi farn ciki da haka ba, wanda kuma tabbas hakan ne ma ya sanya su fara daukar matakai na bangare daya ta fuskar tsaro ba tare da Amurka ba.
Babban abin da bayanin bayan taron na Brussels ya kunsa a jimillance dai shi ne, wajabcin kara hada karfi da karfe tsakanin kasashe mambobi a kungiyar wajen daukar matakai cikin 'yanci ta fuskar tsaro da siyasa a mataki na kasa da kasa, wanda hakan ne ke yin ishara da cewa kungiyar tarayyar turai a shrye take ta yi gaban kanta a wadannan bangarori ba tare da Amurka ba, matukar dai Donald Trump ya tsaya kan bakansa, na kawo karshen yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da kasashen nahiyar turai.