Martanin kungiyar Tarayyar Turai kan sanya Bam a kasar Somaliya
Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alawadai kan harin Bam a kasar Somaliya
A wata Sanarwa da ta fitar a wannan Lahadi, Babbar jami'ar hulda da kasashen waje ta tarayyar turai, Federica Mogherini ta bayyana damuwarta kan ci gaba da kai harin ta'addanci a Magadushu babban birnin kasar Somaliya, wannan sanarwa na zuwa ne a yayin da kasar ke shirye shiryen gudanar da zaben shugaban kasa.
A Jiya Assabar ne aka kai wani mumunan harin Bam da aka makile wata Mota da shi ga wani wurin bincike na Jami'an 'yan sanda dake kusa da wani babban shago da ya kasance mai tsunkoson jama'a a birnin magadushu, harin dai ya yi sanadiyar mutuwar akala mutane 10 tare da jikkata wasu 12 na daban.
Tun bayan da kungiyar Ashabab ta yi mubaya'a da kungiyar ta'addanci ta Alka'ida a shekarar 2012, take daukan nauyin duk wani hare-haren ta'addanci a kasashen Somaliya da Kenya.