Ban Ki Moon ya bukaci a taimakawa masu cutar Kanjamo
(last modified Thu, 01 Dec 2016 11:47:07 GMT )
Dec 01, 2016 11:47 UTC
  • Ban Ki Moon ya bukaci a taimakawa masu cutar Kanjamo

Saktare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci da a taimakawa masu fama da cutar Kanjamo

A yayin dake jawabi na ranar Duniya ta Masu cutar Kanjamo a wannan Alkhamis, Saktare Janar na MDD Banki Moon ya ce wajibi ne a dakatar da rusa masu fama da cutar Kanjamo, a maimakon hakan kamata yayi a taimaka masu ta yadda za su ci gaba da rayuwa ta hanyar amfani da magani da goyon baya na musaman ta yadda za su kawar da damuwar su saboda cutar da suke dauke da ita.

Ban ki Moon ya ce daga cikin manufofin Majalisar Dinkin Duniya , kawar da cutar baki daya a doron Duniya kafin karshen shekarar 2030.

A bangare guda, Michel Sidibe Daraktan gudanarwa na yaki da cutar SIDA na MDD ya ce a halin da ake cikin a kwai milyoyin mutane da suke fuskantar barazanar mutuwa saboda wannan cuta, kuma idan har aka fara gudanar da maganin ta cikin gaggauwa to shakka babu ana iya rage yawan mutuwar mutanan dake kame da cutar da kashi 96%.