Sabon Babban Sakataren MDD: Majalisar Dinkin Duniya Tana Fuskantar Babbar Kalubale
(last modified Wed, 04 Jan 2017 05:54:12 GMT )
Jan 04, 2017 05:54 UTC
  • Sabon Babban Sakataren MDD: Majalisar Dinkin Duniya Tana Fuskantar Babbar Kalubale

Sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa ko shakka babu Majalisar Dinkin Duniyan tana fuskantar babban kalubale a gabanta sakamakon gazawar da ta yi wajen magance matsaloli daban-daban da suka addabi duniya.

Sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bayyana hakan ne a jiya Talata wacce ita ce ranar farko ta fara aikinsa a matsayin sabon babban sakataren MDD inda ya ce a halin yanzu duniya tana cikin rikice-rikice ta kona wadanda suke da alaka da junansu lamarin da ya haifar da sabon kalubale na ta'addanci na kasa da kasa.

Mr. Guterres ya kara da cewa wajibi ne Majalisar Dinkin Duniyan ta yi fada da kuma samo hanyoyin magance wadannan matsaloli da rikice-rikice da suka dabaibaye duniyar, don kuwa a cewarsa Majalisar ta gaza wajen magance da dama daga cikin matsalolin da ake fuskanta din.

A ranar 13 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ta 2016 ne aka zabi Mr. Guterres wanda ya  kasance tsohon firayi ministan kasar Portugal ne a matsayin sabon babban sakataren majalisar duniya da zai maye gurbin tsohon babban sakataren majalisar Ban Ki Moon wanda ya gama wa'adin mulkinsa a ranar 31 ga watan Disambar 2016, wanda kuma da dama suke ganin ya gaza ainun wajen magance mafi yawa daga cikin matsalolin da duniya ta fuskanta tsawon wa'adin mulkinsa.